







“Za kuma a samar da wata karamar cibiyar ruwa ta rijiyar burtsatse a yankin Tabra, da gyara wasu tsoffin hanyoyin ruwa. Za a sanya na’urori da shimfida bututun ruwa masu nisan kilomita 160 a cikin birnin da kuma sanya na’urorin kula da cibiyoyin ruwa guda 100, da gyaran bawulan ruwa 100 da ake da su,” kwamishinan yace akalla mitocin ruwa na zamani 2000 za a samar a farkon shirin samar da mitocin.
Da yake bayanin ci gaban kungiyar, ya ce tuni aka kafa kwamiti karkashin jagorancin Mataimakinsa, Musa Jibrin Tabra, kuma nan ba da jimawa ba, kwamitin zai bada rahotonsa, wanda kungiyar za ta duba shawarwarin tare da aiwatar da su don habaka aikace-aikacen kungiyar.
Mijinyawa Yahaya ya bayyana cewa sauran wuraren da kwangilar zata shafa sun hada da gina karamar tashar ruwa a Tabra, da gyara hanyoyin ruwan, da shimfida bututun rarraba ruwan na kusan kilomita 160 a cikin babban birnin Gombe da kuma kafa cibiyoyin budewa da rufe ruwa guda 100 da kuma gyara wadanda ake dasu.












