Chen Wanghui, ita ce sakatariyar reshen JKS a kauyen Maoshui na gundumar Xiaojin na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin. Cikin shekaru 10 da suka gabata, ta jagoranci mazauna kauyen wajen yaki da talauci ta hanyar noman furannin Rose, lamarin da ya kai su ga sauya gundumar Xiaojin zuwa sansanin noman Rose mafi inganci da girma a fadin kasar Sin. Chen ta dukufa wajen hada raya kasuwancin Rose da aiwatar da aikin farfado da kauyen, a matsayin wata hanya ta zamar da Xiaojin wuri mai kyan gani. Mutanen kauyen na kiranta da Sarauniyar Rose ko kuma Sakatariyar Rose saboda yabawa taimakon da ta yi musu.






Yayin wani rangadin duba tsirran da aladun daji suka lalata, Chen ta lura da wasu furannin Rose a gonakin, nan da na kuma ta fahimci cewa, furannin na iya tsirowa da kyau saboda ganyensu mai kaya. Baya ga haka, yadda Maoshui ke yanki mai tsawo da kuma rana mai karfi a yankin, ya sa shi dacewa da samar da ingantattun furannin Rose.
Bayan wannan sabon nau’in Rose ya samu karbuwa a kasuwa, sai Chen ta sarrafa su zuwa miya da ganyen shayi, kuma ta ba wata masana’anta dake birin Lanzhou aikin matse man furen Rose.
A cewar Chen, yara da manya duka na iya girbin furannin Rose. Kuma a karkashin jagorancinta, wasu jami’an kauyen da mazaunansa, sun fara shuka furannin.












